Yaki da aiyyukan ta´adda a Masar
May 9, 2006Talla
Yan sandan kasar Masar sun harbe shugaban kungiyyar tsagerun matasan da suka kai harin bam a yankin Sinai na yan yawon shakatawa.
A cewar rahotanni, yan sandan sun harbe Naseer Khamis Al Mallahi ne, bayan wani dauki ba dadi daya wanzu a tsakanin yan kungiyyar su ta Tawhid Wal Jihad da kuma jami´an tsaron.
Bugu da kari, jami´an tsaron sun kuma sami galabar cafke na hannun daman shugaban kungiyyar ta Tawhid wal Jihad, wato Mohd Abdalla Elian.
Idan dai za´a iya tunawa an zargi yan kungiyyar ta Tawhid wal Jidad din ne da kai harin bam a Dahab a watan afrilun daya gabata, wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwar yan yawon shakatawa 19.