YAKI DA ADDABAR MATA A DUNIYA. | Siyasa | DW | 25.11.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

YAKI DA ADDABAR MATA A DUNIYA.

Idan aka kwatanta halin rayuwar jama'a a nan Jamus, da na wasu wurare daban-daban na duniya, sai a ga cewa, har ila yau ana zaman walwala da lumana a nan kasar. Mafi yawan al'umman Jamus dai sun yi karatu mai zurfi, ko kuma suna da wata sana'a, wadanda ke ba su damar samun ayyukan yi don tafiyad da halin rayuwarsu, kamar yadda suka ga ya fi dace musu. Marasa galihun ma, `yan gata ne idan aka kwatanta su da na wasu kasashen. Saboda akwai kafofin hukuma da kuma taimakon da gwamnati ke bayarwa, don kula da wannan nau'in na al'umman kasar.
Amma duk da haka, a nan Jamus din ma, ana samun karin yawan sabani da rikice-rikice tsakanin iyalai. A galibi, tashe-tashe hankullan da ke barkewa a gidajen iyalan, a kan matan gidan ne suke karewa. Wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar, ya nuna cewa, ko wace mace daya cikin uku a nan Jamus, mai sama da shekaru 16 da haihuwa, ta taba shan duka ko kuma dai wata azaba a hannun wani namiji a gidansu, ko ubanta, ko mijinta, ko kuma saurayinta, in suna zaman tare ne. Wasu matan ma na kamuwa da cututtuka saboda addabarsu da maza ke yi. Amma ko saboda tsoro, ko kuma rashin amincewa da kansu, da yawa daga cikin matan ba sa iya kai wani, ko da ma `yan uwansu ne, karar abin da mazajensu ke yi musu.
Wata dokar da gwamnatin tarayya ta zartar a nan Jamus a cikin shekara ta 2002, ta inganta matsayin mata a a kann wannan batun, ta kuma ba su damar kai karar mazajen da ke yi musu duka ba gaira ba dalili gaban shari'a. Don kuma kada a ce ana nuna wariyar jinsi a gaban shari'a, mazan ma za su iya kai karar matansu, idan matan ne suka yi musu duka. Amma alkaluma na nuna cewa, a galibi dai, matan ne suka fi galabaita a hannun maza.
Wasu manazarta halin rayuwar jama'a sun gudanad da wani bincike, inda suka gano cewa, matsin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu, da damuwar da jama'a ke yi na rasa guraban aikinsu a kamfanoni, da kuma dai rashin iya huskantar kalubalen da canje-canjen da ake samu a duniya ke janyowa. Tabarbarewar halin tattalin arzikin jama'a da rashin amincewa da kansu, na cikin dalilan da ke haddasa wasu halaye na cin zalin mutane. Kamar dai yadda binciken ya nunar, maza ne suka fi damuwa da matslolin halin rayuwa, sabili da haka ne kuma, suka fi addabar abokan zamansu mata. Alkaluma kuma sun tabbatad da wannan ra'ayin. Kusan kashi 90 cikin dari na duk wadanda ake tuhumarsu da laifin kisa a nan Jamus, maza ne.
Wani rahoton da Asusun Mata na Majalisar dinkin Duniya, wato UNIFEM ya buga na nuna cewa, ana kara samun habakar cin zalin mata da maza ke yi a duniya baki daya. Noeleen Heyzer, shugaban wannan Asusun, ta bayyana a birnin New York a kwanakin baya cewa, addabar da ake yi wa mata a duniya ta zamo kasmar wata annoba. Ban da danne musu hakki da ake yi a cikin gidajensu, habakar fataucin da ake yi da mata a kasashen duniya, a galibi inda ake tilasa musu yin karuwanci, na cikin ababan da suka fi damun shugaban asusun. A ko wace shekara dai, kusan mata dubu dari 7 ne ake fataucinsu, inda kuma ake nuna musu azaba iri-iri, da yi musu fyade da kuma cin zarafinsu. Sabili da hhakan ne kuwa, mafi yawansu ke kamuwa a sawwake da cutar nan ta AIDS.
Kamar dai yadda Kofi Annan, babban sakataren Majalisar dinkin Duniya ya bayyanar, a cikin jawabinsa na bikin ranar juyayi ga addabar da ake yi wa mata a duniya, maza na da muhimmiyar rawar takawa, wajen ganin cewa, an kau da wannan cin zarafin da ake yi wa mata daga doron kasa. Don cim ma wannan gurin kuwa, kamata ya yi mazan su nuna bajinta wajen sake halayyansu dangane da matsayin da suke bai wa mata, inji Annan.
 • Kwanan wata 25.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnR
 • Kwanan wata 25.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnR