1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yajin aikin yini guda a Zimbabwe

Shugaba Robbert Mugabe na Zimbabwe

Shugaba Robbert Mugabe na Zimbabwe

Jamian tsaro sun mamaye birnin Harare cikin shirin kota kwana,domin kalubalantar zanga zangar da kungiyoyin jamaa suka shirin gudanarwa a yau sakamakon hali na kuncin rayuwa da suke fuskanta.

Jamian yansanda dauke da makamai naciga da shiga sako sako a fadar gwamnatin zimbabwe ta Harare,tare da bincike jikin mutane da motoci,kamar yadda ake cigaba da gudanarwa a sauran manyan biranen wannan dake kudancin Afrika.

Masu shirya wannan bore daga babbar kungiyar kwadagon kasar sunyi fatan cewa dubban alummar kasar ne zasu fito domin gudanar das wannan zanga zanga,ta hanyar watsi da haramta musu izini da akayi,a sassa daban daban na kasar.

Ana dai ganin cewa wannan gangamin zai zame na farkon irinsa da yan adawan kasar zasu samu gudanarwa ayau din,tun bayan da babbar jammiyar adawa ta MDC ta dare biyu a watan Nuwamban daya gabata.

Babban sakataren kungiyar maaikatan na Zimbabwe Wellington Chibebe,ya hakikance cewa ,babu gudu babu jada baya a dangane da wannan bore da suka shirya gudanarwa ayau,duk da watsa jamian tsaro da akayi akan tituna,koda yake kungiyoyi biyu ne har yanzu suka hakikance shiga wannan wannan yajin aiki.

To sai dai lokaci kalilan gabannin fara wannan gangamin,babu wasu alamun dake bayyana cewa zaa samu nasaran fitowan mutane.

Wani dan kasuwa mai suna George Kuriyati,ya bayyana cewa jamaa a zimbabwen na tsoron fitowa,kana a hannu guda kuma suna fafutukar samun abunda zasu kai baka,asabilida haka idan akwai masu shiga wannan zanga zangar ma ,mutane kalilan ne.

A kasar da Zimbabwe yanzu dai mutane na tsoron martanin gwamnati dangane da shiga yajin aiki,saboda yadda jamian tsaro ke gallazawa wadanda akan cafke azaba.

Bugu da kari mafi yawa na ganin cewa babu wani tudun dafawa da zaa cimma ta hanyar yajin asiki,musamman bisa laakari da wadanda suka sha gudanarwa a baya,domin kwalliya bata mayar da kudin sabulu ba.

Kungiyar kwadago mafi girma a zimbabwen watau ZCTU dai,na neman karin albashi ne wa maaikata,bisa ga laakari da yadda ake dada samun tsadar rayuwa,da kuma rage musu yawan yanke haraji.

Kazalika kungiyar na kira da a a kawo karshen cigaban kame kamen da dukan masu tallace tallacen kaya akan tituna,da wadanda ke gudanar da kasuwancin kansu.

A bangaransa,sakatare general na jammiyar adawa ta MDC Tendai Biti,yace jammiyarsu zata bada goyon bayanta wa yajin aikin 100 bisa 100.

A shekarun baya dai yajin aiki makamancin wanbnan da kungiyoyin kwadagon ke gudanarwa,a karkashin jagorancin shugaban Adawa Morgan Changirai, ya sha barazanar durkusar da harkokin tattalin arzikin zimbabwen dake kudancin Afrika.

 • Kwanan wata 13.09.2006
 • Mawallafi zainab A Mohammad.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtyD
 • Kwanan wata 13.09.2006
 • Mawallafi zainab A Mohammad.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtyD