Yajin aikin matuka jiragen kasa a Jamus | Labarai | DW | 07.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin matuka jiragen kasa a Jamus

Matuka jiragen kasa zasu shiga yajin aiki

Matuka manyan jiragen kasa na nan tarayyar jamus zasu sake shiga yajin aiki.A wannan karon kungiyar matuka jiragen ta GDL,zasu shiga yajin aikin ne daga misalin karfe 12 na ranar gobe alhamis,wanda zai dauki sao’i 42 yana gudana,kamar yadda shugaban kungiyar Manfred Schell ya bayyana….

„Daga ranar alhamis na wannan makon da rana manyan jiragen pasinja zasu shiga wani zagayen yajin aiki,har zuwa ranar Asabar da misalin karfe 6 na safe“

Wakilan kungiyar ta GDL dai sun yi watsi da kiran komawa teburin tattaunawa da magabatan kamfanin jiragen kasa ta Deutsche Bahn.Wannan yajin aiki da matuka jiragen kasan zasu shiga dai,zai janyowa kamfanin asarar kudaden shiga na kimanin Euro milioon 50,ayayinda zai hana kamfanoni da dama sarrafa kayayyakinsu.