1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin matuƙan jiragen ƙasa a Jamus

November 15, 2007
https://p.dw.com/p/CE7F

Matuƙan jiragen ƙasa a nan Jamus sun zurfafa yajin aikin da suka fara na saói 62 lamarin da ya haifar da tsaiko ga zurga zurgar fasinjoji da kuma safarar manyan kaya sakamkon takamma tsakanin direbobin jiragen da kamfanin sufuri na Deutsche Bahn. ƙungiyar matuka jiragen ƙasan ta umarci dukkanin`ya´yan ta waɗanda ke tuka jiragen fasinja na dogon zango su bi sahu wajen wannan yajin aiki. Wannan dai shine yajin aiki mafi taázzara a tarihin harkokin sufurin jiragen ƙasa a nan Jamus. Yajin aikin wanda ya fara tun daga ranar laraban nan da kuma za ta kai har zuwa ranar Asabar, ya raunana harkokin zurga zurgar jamaá. A halin da ake ciki kamfanin sufurin na Deutsche Bahn ya tsara jadawalin harkokin sufurin na wucin gadi zuwa ƙarshen mako. Babu dai alamu na cimma yarjejeniya da direbobin ta samun masalaha a kan bukatun su na ƙarin albashi.