Yajin aikin ma′aikatan Opel | Zamantakewa | DW | 05.11.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yajin aikin ma'aikatan Opel

Ma'aikatan kamfanin sarrafa motoci na Opel su dubu 25 suka dakatar da aiki domin adawa da shawarar kamfanin na janyewa daga cinikin da aka ƙulla da kamfanin Magna a zamanin baya

default

Ma'aikatan Opel dake yajin aiki na gargaɗi

Kimanin ma'aikata na kamfanin Opel dubu 25 suka dakatar da aiki na ɗan gajeren lokaci domin adawa da kamfanin General Motors na Amurka. An shirya wannan zanga-zangar ce a garuruwan da kamfanin na Opel ke da reshensa a duk faɗin Jamus. Manufarsu game da wannan mataki shi ne domin Allah Waddai da shawarar da kwamitin zartaswa na kamfanin ya tsayar na hana sayar da kamfanin Opel ga kamfanin Magna mai sarrafa kayayyakin harhaɗa motoci. A maimakon haka kamfanin na GM na fatan sabunta al'amuran Opel ne da kansa.

A dai halin da ake ciki yanzun an ƙayyade wa kamfanin General Motors wa'adin nan da ƙarshen wata domin mayar da rancen Euro miliyan dubu ɗaya da ɗari biyar da aka ƙaddamar da farkon fari don taimaka masa daga mawuyacin halin da ya samu kansa a ciki. To sai dai kuma ba wanda ya san tahaƙiƙanin manufar kamfanin na General Motors a game da makomar Opel yanzu haka. Duka-duka sanarwar da aka samu daga wajensa shi ne yana buƙatar tsabar kuɗi Euro miliyan dubu uku don sabunta al'amuransa baki ɗaya. In banda haka babu wani bayani dalla-dalla da aka samu. Wannan ya jefa shugaban reshen gudanarwa na kamfanin Klaus Franz ya shiga lalube a cikin dufu:

"Muna dai da cikakkiyar masaniya a game da ƙudurin da General Motors ya tsayar a zamanin baya, wanda ya haɗa da rufe wasu rufumfunan sarrafawa guda uku a nahiyar Turai da dakatar da dubban ma'aikata a wata fuska ta dabam, kamar yadda lamarin ya kasance dangane da kamfanin Magna da kuma Sberbank. To ko Ya-Allah za a ci gaba da aiwatar da wannan shirin, a yanzun ba abin da zan iya cewa game da haka. A sakamakon hakan ne muke cikin wani mawuyacin hali na rashin sanin tabbas."

A dai halin da ake ciki yanzu General motors ya sanar da cewar zai dakatar da ma'aikata dubu 10 daga cikin ma'aikata dubu 50 na kamfanin Opel a faɗin Turai. Sai dai kuma a yayinda ake neman bakin zaren warware matsalar dangane da rassan kamfanin na Opel a garuruwan Bochum da Eisenach dake nan Jamus, babu wani haske a game da reshensa na Antwerps dake Belgium, kamar yadda aka ji daga manejan General Motors John Smith. A nasa ɓangaren Christoph Stürmer ƙwararren masani a cibiyar ba da shawara ta Global Insight ya ce ba makawa game da rufe wasu rassa na kamfanin:

"Bisa ga dukkan alamu ba makawa game da rurrufe wasu ma'aikatun, saboda tsadar ayyukan sarrafawa a nahiyar Turai, lamarin da kamfanin General Motors ke nazari kansa a halin yanzu haka."

Klaus Franz shugaban kwamitin ayyukan sarrafawa na Opel ya ce za a ci gaba da nemo wasu kamfanonin da zasu iya mayewa gurbin kamfanin General Motors, sai dai kuma bai yi wani ƙarin bayani ba. Bisa ga dukkan alamu dai a yanzun bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi tsawon watanni da dama dukkan sassan biyu na yi wa juna kallon hadarin kaza ne. Amma fa wajibi ne dukkan ɓangarorin biyu su fahimci cewar komawa kan teburin shawarwari shi ne kaɗai zai taimaka a samu bakin zaren warware wannan matsala.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu