Yajin aikin ma´aikatan BA | Labarai | DW | 30.05.2010
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin ma´aikatan BA

Ma´aikatan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na British Airways sun shiga yajin aikin kwanaki biyar

default

Yajin aikin ma´aikatan BA

Ma´aikatan kamfanin zirga zirgar jiragen sama na British Airways sun shiga wani saban yajin aiki na kwanaki biyar.Ranar Juma´ar da ta wuce ne, aka watse baran-baran tsakanin Ƙungiyar ma´aikatan da hukumomin  kamfanin British Airways.Suna zargin Babban manajan kamfanin Willie Walsh da saka tarnaƙi ga tattanawar da suka shirya.

Cemma a  watan Maris da ya gabata, sun yi yajin aikin kwanaki bakwai, wanda ya jawo asara fiye da Euro miliyan 50 ga kamfanin British Airways.

Ma´aikatan sun ce da zaran dai haƙar ba ta cimma ruwa ba, zasu shiga wani saban yajin aiki ranar biyar ga wata mai kamawa, abinda bisa dukkan alamu zai iyxa kawo cikas ga matafiya agasar cin kofin ƙwallan ƙafa ta duniya,da zata fara ranar 11 ga watan Juni a Afrika ta Kudu.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Halima Balaraba Abbas
 • Kwanan wata 30.05.2010
 • Mawallafi Sadissou Yahouza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/NdIK
 • Kwanan wata 30.05.2010
 • Mawallafi Sadissou Yahouza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/NdIK