Yajin aikin maáikata a Nigeria | Labarai | DW | 22.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin maáikata a Nigeria

Ƙungiyoyin ƙwadago a Nigeria sun lashi takobin cigaba da yajin aikin sai baba ta gani na ƙin amincewa da ƙarin farashin mai a ƙasar ta Nigeria mafi arzikin mai a nahiyar Afrika. Tattaunawar da aka shafe tsawon daren jiya ana gudanarwa tsakanin wakilan gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadagon da nufin kawo ƙarshen yajin aikin ta ci tura, inda aka tashi baran baran ba tare da cimma wata masalaha ba. Yajin aikin ya kassara harkokin tattalin arziki a Nigeriar wadda ke zama ƙasa ta takwas da suka fi arzikin mai a duniya. Sai dai yajin aikin baá kai ga tsayar da hakowa da kuma fitar da man zuwa ƙetare ba. Gwamnatin Nigeriar, ta ce ba zata lamunta da kange hanyoyi da kuma barazanar da yan ƙwadagon ke yi ba, matakin da ake gani zai ƙara haifar da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin maáikatan da gwamnati. Dambarwar yajin aikin dai ta hana sabon shugaban ƙasar Umaru Musa Yar Aduá sukuni wanda ya gaji matsalar ƙarin farashin man daga tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo. Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta Nigeria NLC Abdulwahid Omar yace za su cigaba da yajin aikin har sai abin da hali yayi matuƙar gwamnatin bata cire ƙarin farashin man ba.