Yajin aikin jiragen kasa a Jamus | Labarai | DW | 25.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin jiragen kasa a Jamus

Yajin aikin sa’i 30 da maaikatan kamfanin jiragen kasa na tarayyar jamus ke gudanarwa a yau ,ya haifar da tsaiko cin harkokin tafiye tafiye asassa daban daban.Hukumar jiragen kasar ta Deutsche Bahn ,ta bayyana cewar lamarin yafi muni a yankin gabashin Jamus,ayayinda a yankin yammacin kasar kuwa,rabin jiragen ne suke yin zirga zirga,kamar yadda wani jami’in kamfanin jiragen Karl-Friedrich Rasch yayi bayani…

„Yace yanayin ,kamar wanda akayi a baya ya jefa pasinjoji cikin hali mawuyaci.Matsalar a wannan karon yafi muni saboda tsawon saoi 30 zai dauka ana yajin,tun jiya da maraice muke tattaunawa da wakilan kunguyar matuka jiragen na GDL,adangane da haramta musu wannan yaji da kotu tayi,“

Wannan yajin aiki dai zai cigaba zuwa saoin cunkoson safe na gobe juma’a.