Yajin aikin gama gari ya samu karbuwa a Chadi | Labarai | DW | 29.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari ya samu karbuwa a Chadi

Hadin gwiwar kungiyoyin kwadago a sun kira yajin aikin da ya samu karbuwa a kabuwa a kasar Chadi, inda ma'aikatu suka kasance rufe.

Yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka kira na neman a saki wasu shugabannin kungiyoyin fararen hula hudu da aka kama ya samu babbar karbuwa. Ma'aikatu daban-daban sun kasance a rufe, har da babban gidan shari'a na kasar ba a yi shari'a ko daya ba, sannan kuma ma'aikata ba su yi aiki ba a babban asibitin birnin na Ndjamena fadar gwamnatin kasar.

Daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Younous Mahadjir, na a matsayin shugaban wani sashe na babban asibiti birnin, kuma an kama shi ne yayin da yake a bakin aikinsa, inda gaba daya ake zarginsu da laifin neman tada zaune tsaye. Kungiyoyin dai na nuna adawarsu da sake tsaya wa takara da shugaban kasar Idriss Deby Itno ya yi, duk kuwa da cewa ya shafe tsawon shekaru kusan 26 yana mulkin kasar ta Chadi.