1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari a kasar Habasha

Yan adawa a kasar Habasha sun yi barazanar gudanar da yajin aiki na gama gari har tsawon mako guda domin nuna bacin rai ga abin da suka kira tabarbarewar alámura a kasar. An ruwaito cewa Kantuna a babban birnin kasar Addis Ababa sun kasance a rufe. Yan adawar na korafi a game da sakamakon zaben majalisun dokoki da aka gudanar a kasar a watan Mayun da gabata wanda suka ce an tafka magudi a cikin sa. A waje guda kuma gwamnatin ta kame wasu shugabanni ashirin da hudu na yan adawar ba tare da tuhuma ba.