Yajin aikin gama gari a kasar Faransa | Labarai | DW | 28.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari a kasar Faransa

A kasar Faransa alámura sun tsaya cik a sakamakon yajin aiki na gama gari da kungiyoyin kwadago dana dalibai suka fara a yau din nan domin tilastawa P/M kasar Dominique de Villepin yin watsi da sabuwar dokar kwadago ta daukar matasa aiki. Jamaá sun yi carko carko musamman a birnin Paris inda aka sami tsaiko na harkokin sufuri. An soke tashi da saukar jirage a filin jirgin sama na Lyon dake kudancin kasar ta Faransa. Gagarumin yajin aikin gamarin wani babban kalubale ne ga P/M Dominique de Villepin wanda ke neman tsayawa takara a zaben da zaá gudanar a kasar Faransa a shekara mai zuwa.