1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari a ƙasar Guinea

Ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar Guinea dake yammacin Afrika a ranar litinin din nan suka cigaba da yajin aikin gama gari bayan tarzoma a ƙarshen mako wanda ya hallaka a ƙalla mutane goma sha ɗaya.

Shugabannin ƙwadagon na buƙatar shugaban ƙasar Lansana Conte ya yi murabus. A ƙarshen mako Shugaba Lansana Conte ya naɗa sabon P/M kamar yadda yan ƙwadadagon suka buƙata, to amma sai ya naɗa wani tsohon Aminin sa a kan wannan matsayi.

Sakatare janar na kungiyar ƙwadagon Ibrahim Fofana yace ko kaɗan ba za su amince da naɗin P/M ba.