Yajin aikin Direbobin jiragen kasa a Jamus | Labarai | DW | 06.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin Direbobin jiragen kasa a Jamus

Direbobin dake kula da manyan jiragen kasa dake tarayyar jamus,sun kada kuriar amincewa da kaddamar da yajin aiki na bayyana kokensu wa kamfanin jiragen ,da ake kira Deutsche Bahn AG.Kungiyar direbobin a wata sanarwar data gabarat,ta nunar dacewa sakamakon kuriun da wakilanta su dubu 12 suka kada,yayi nuni dacewa,sun amince da da shiga wannan yajin aiki,adaidai lokacin da ake gudanar da hutu ,kuma harkokin yawon shakatawa yake yawaita.Tuni dai gwamnatin tarayyar jamus ta jaddada bukatar shawo kann wannan matsala kafin direbobin su fara wannan yajin aiki,wanda zai kawo koma baya cikin harkokin tattalin azrikin wannan kasa mai yawan mazauna milion 82,wadda kuma tafi karfin tattalin arziki a nahiyar turai.