Yajin aikin abubuwan sufuri ya kawo cikas a New-york | Labarai | DW | 22.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin abubuwan sufuri ya kawo cikas a New-york

Wani Alkali a birnin New York dake Amurka yace da alama shugabannin kungiyar sufuri na birnin ka iya fuskantar hukunci na dauri a gidan yari bisa kiran da sukayi na a shiga yajin aiki.

Ya zuwa yanzu a cewar rahotanni da suka iso mana, tuni wata kotu taci tarar shugabannin sufuri na birnin, dalar Amurka miliyan daya ako wace rana da aka shiga ana yajin Aikin, bisa hujjar cewa dokar birnin ta hana ma´aikatan sufuri shiga yajin aiki.

Yayin da wannan yajin aiki ya shiga kwana na biyu, da yawa daga cikin mutanen birnin naci gaba taka sayyadar su izuwa guraren hada hadar yau da kullum, wasu kuma subi motoci na yan uwa da aboka nan arziki.

Bayanai dai sun nunar da cewa ako wace rana aka shiga ana wannan yajin aiki, birnin na New york na yin asarar Dalar Amurka miliyan 400.