Yajin aikin ƙungiyoyin drebobin jiragen ƙasa a Jamus. | Labarai | DW | 05.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin ƙungiyoyin drebobin jiragen ƙasa a Jamus.

An watse baran-baran a tantanawar da a ka shirya tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago na matuƙan jiragen ƙasa da kampanin Deutsche-bahn mai kulla da zirga zirga da jiragen ƙasa a Jamus.

Tun ranar litinin da ta wuce, drebobin jiragen su ka shiga yajin aiki, domin cilastwa kampanin Deutsche Bahn, ya biya masu buƙatoci su,da su ka haɗa da ƙarin albashi.

Ya zuwa yanzu, kampanin ya ƙara kashi 2 bisa 100 , a yayin da ƙungiyoyin ma´aikatan ke buƙatar kashi 7 bisa 100.

A tantanawar da ɓangarorin 2 su ka yi yau, kampanin Deutsche Bahn ya alkawarata karin kashi 3, 4 bisa 100, yan ƙwadagon su ka yi watsi da shi.

Taron ya watse baran-baran, sai kuma ranar lahadi idan mai duka ya so.

Saidai kamin nan ƙungioyin matuƙa jiragen, sun yanke shawara ci gaba da yajin aiki.