1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki a Portugal

November 24, 2010

A ƙasar Portugal an shiga yajin aiki don nuna adawa da shirin gwamnati na tsuƙe bakin aljihu.

https://p.dw.com/p/QHPY
'Yan zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuƙe bakin aljihu.Hoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Portugal yajin aikin adawa da shirin tsuƙe bakin aljihun gwamnati na sa'o'i 24 da aka fara ya tsai da komai cik. Baki ɗayn ma'aikatan gwamnati da na masu zaman kansu suka shiga yajin aikin. Jiragen sama da na ƙasa da motocin kwasan shara da tashoshin jiragen ruwan duk sun rufe wuraren ayyukansu. a tsawon yinin yau. Wannan yajin aikin shi ne na farko tun shekaru da ya samu haɗin kan ma'aikata masu zaman kansu da na gwamnati. Gwamnatin ƙasar a shirinta na tsuƙe bakin aljihu, ta na son ƙara haraji kan kayan da ake sayarwa da kashi biyu cikin ɗari, kana za ta riƙe kuɗin fansho duk a ƙoƙarin da take yi na cika ƙa'idar ƙasashen Ƙungiyar Tarayar Turai da asusun ba da lamuni ta duniya wato IMF.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas