Yajin aiki a Faransa ya dumama harkoki na siyasa a kasar | Labarai | DW | 04.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aiki a Faransa ya dumama harkoki na siyasa a kasar

Rahotanni daga faransa na nuni da cewa an samu jinkirin sufuri na zirga zirgar jiragen sama da kuma cunkoson abubuwan hawa ada yawa daga cikin biranen kasar.

Hakan kuwa ya samo asali ne bayan da kungiyoyin kwadago dana yan makaranta suka fara wani yajin aikin sai baba ta gani, don nuna adawar su qa game da sabuwar dokar nan ta daukar aiki.

Dokar wacce ta samu amicewar shugaba Jack Chirac, ta bawa kamfaninnika da masana´antu dama na daukar ma´aikata tare kuma da korar su, bayan gabatar musu da kwararan hujjoji.

Ana dai sa ran mutane a kalla miliyan daya ne zasu gudanar da wata gagarumar zanga zanga a kasar don nuna adwar su da wannan sabuwar doka.

Ya zuwa yanzu dai tuni, jami´an tsaro suka kasance a cikin shirin kota kwana, musanmamma a birnin Paris don dakile duk wata fitina daka iya tasowa, a lokacin zanga zangar.