Yajin aiki a birnin Newyork na kasar Amurka | Labarai | DW | 20.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aiki a birnin Newyork na kasar Amurka

Yajin aikin da ma´aikatan sufuru na jiragen kasa da kuma Bus Bus suka shiga a Birnin Newyork na kasar Amurka ya jefa miliyoyin mazauna birnin cikin hali na ni yasu.

Yajin aikin daya zo a dai dai lokacin da ake shirye shiryen gudanar da bukukuwan kirsimeti, an shaidar da cewa ako wace rana ta yajin aikin ana asarar dalar Amurka ne miliyan 400.

Kungiyyar ma´aikatan sufurin dai ta kira wannan yajin aikin ne, don bukatar karin albashi da kuma irin kudaden da ake bawa ma´aikata bayan sunyi ritaya.

Wannan yajin aiki dai na a matsayi n irin sa na farko ne a birnin na Newyork a tsawon shekaru 25.