Yajejeniyar Schengen | Siyasa | DW | 25.03.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yajejeniyar Schengen

A misalin shekaru 10 da suka wuce yarjejeniyar nan ta Schengen dake kawar da shinge tsakanin iyakokin kasashen Turai ta fara aiki

A dai halin da ake ciki yanzu kusan dukkan al’umar kasashen Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) ke da ikon kai da komo ba tare da an biciki takardunsu ba sai dai kawai idan zasu fita ko zasu shigo wata kasa ta kungiyar daga ketare. Duka-duka '‚an kasashen Birtaniya da Irland ne ke nuna takardunsu na fasfo a lokacin da suka tsallako daga tsuburinsu zuwa nahiyar Turai. Kasashen biyu sun ki su shiga inuwar yarjejeniyar ta Schengen ne saboda matsayinsu na tsuburi, a yayinda kasashe kamar Norway da Island ke cikin yarjejeniyar duk da cewar ba su da wakilci a KTT. Dubban daruruwan mutane ke kai ziyara kauyen Schengen mai mazauna 400 a kasar luxemburg saboda muhimmancinsa a tarihin hadin kan Turai. A lokacin da yake bayani game da haka, magajin garin Schengen Roger Weber ya bayyana farin cikinsa a game da yadda ake danganta wannan yanki da ‚yancin shige da fice tsakanin illahirin al’umar Turai. Weber ya kara da cewar:

Muna alfahari da kasancewar an rattaba hannu kan yarjejeniyar ta shige da fice a nan Schengen. Kuma duk da cewar abin ya zo ne a ba zata, amma muna alfahari da haka.

A wancan lokaci kasashe biyar dake da hannu a yarjejeniyar, wadanda suka hada da Jamus da Faransa da Holland da Belgium da kuma Luxemburg suka hallara domin kaddamar da wannan biki. An zabi kasar ta Luxemburg ce saboda ita ke rike da shugabancin KTT a lokacin. A dai wannan halin da muke ciki yanzun yarjejeniyar ta Schengen ta zama wata madogara da kasashen Turai ke alfahari da ita a kokarin tabbatar da kan nahiyar. Sabbin kasashen da suka shigo karkashin tutar kungiyar baya-bayan nan na fatan ganin an gaggauta kawar da shigen dake akwai a iyakokinsu, kuma kungiyar zata taimaka musu da kudi wajen kyautata al’amuran tsaron iyakokinsu na wajen kungiyar. To sai dai kuma, kamar yadda manazarta ke gani, wannan dama ta shige da fice ba tare da binciken takardun fasfo ba ta share wa miyagun mutane fagen cin karensu babu babbaka, a yayinda a daya bangaren mahukunta na ‚yan sanda ba su da wata dama shige da fice tsakanin kasashen da lamarin ya shafa a kokarinsu na farautar masu miyagun laifuka.