1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yahudawan Iran sun koma Israila

Ayarin iyalai goma na yahudawa sun isa Isaraila daga ƙasar Iran. Wannan shine ayari mafi yawa da suka bar Iran tun juyin juya halin ƙasar na 1979.Bisa dukan alamu wadannan iyalai sun bar dukan abin da suka mallaka a ƙasar ta Iran.A wannan shekara kadai,Yahudawa dari biyu ne suka bar Iran. Yahudawa kimanin dubu 25 ne ke zaune a kasar ta Iran.Shugaban Iran, Mahmud Ahmadinejad ya shan yin kira da a tarwatsa Israila.