1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaduwar cutar murra tsintsaye a dunia

February 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6Z

Cutar murra tsintsaye na shirin zama gagarabadau, ga hukumomin kiwan lahia na dunia.

Bayan ƙasashe 6, na ƙungiyar gamayya turai, da su ka riga su ka kamu da wannan cuta, a yau, an samu rahoton ɓullar ta, a kasar Sueden.

Jamus, na ɗaya daga ƙasashen ƙungiyar gamaya turai da cutar da fi bazuwa.

Ya zuwa yanzu, jihohi 5 daga jimilar jihohi16 na ƙasar su ka kamu da wannan cuta.

A jimilce, agwagi 130 ne, a ka tabbatar da sun mutu, a sanadiyar murra tsintsaye, a nan kasar Jamus, saidai har yanzu, ba a samu goguwar ta ba, daga tsintsye zuwa bani adama.

A nahiyar mu ta Afrika, bayan Taraya Nigeria, da Masar, an tabbatar da cutar ta isa Jamhuriya Niger.

Sannan a na kauttata zaton, ta kai ƙasar Ethiopia, inda kaji dubu 6, su ka mutu.

A halin yanzu, ƙurrarun cibiyoyin bincike na ƙasashen turai, na gudanar da bincike don gano sanadiyar mutuwar wannan tarin kaji.