1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YADDA TARON KASAR AMURKA DA KASASHEN LATIN YANKIN YA KASANCE.

January 14, 2004

A daren jiya talata ne dai aka kawo karshen taron kolin wuni biyu a tsakanin kasar Amurka da kasashen Latin na Amurkan da aka gudanar a birnin Monterrey na kasar Mexico.

https://p.dw.com/p/Bvma
A karshen taron na wuni biyu shuwagabannin da suka halarci taron 33 da suka fito daga sako sako da kuma lungu lungu a latin na Amurka sun cimma yarjejeniyar gudanar da kasuwanci a tsakanin juna ba tare da samun wani cikas ba.
Bugu da kari batutuwan da wannan taro ya cimma yarda a kansu kuwa sun hadar da yaki da cin hanci da kuma rashawa da yaki da yan taadda da kuma bunkasa kananan masana ,antu na yankin don suyi gwagwarmaya da manya manyan kamfaninnika da kuma masana,antu na duniya. Ragowar batutuwan kuwa sun hada da yafe basussuka da manyan kasashe na kungiyyar ke bin kana nan kasashe tare da taimakawa tattalin arzikin kasashen matalauta farfadowa ta yadda za,a samo rage radadin fatara daga mutanen kasar.
To amma kuma a hannu daya shuwagababbin kasar Brazil Lula de Silva dana Venezuela Hugu Chaves basuji dadin wannan yarjejeniya da aka cimma ba,musanmamma a kann gudanar da harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen.
Shuwagabannin wadan nan kasashe biyu sun nuna rashin amincewar su da wannan mataki da aka dauka ne kann dalilin su na cewa batun baya daya daga cikin manya manyan jigon da taron na wuni biyu zai tattauna a kann sa.
A don haka suna ganin cewa,batzun ya samu karbuwa ne tare da ingizo daga mahukuntan kasar Amurka,wanda kuma hakan suke ganin za,aci ne kawai da gumin su idan anzo gudanar da harkar kasuwancin a aikace.
Bugu da kari shuwagabannin biyu sun koma soki lamirin wannan mataki da aka dauka da cewa a tsarin baya da kasashen suka yarda akan sa shine za,a dauki mataki na karshe kann wannan batu na kasuwanci a tsakanin kasashen a farkon watan janairu na shekara ta 2005 mai zuwa idan Allah ya kaimu.
Wan nan dai mataki a cewar shuwagabannin na Brazil da Venezuela an cimma masa ne a karshen taron kasashen da aka gudanar a shekara ta 1994 a birnin Miimi na kasar Amurka.
A dai ganin wadan nan shuwagabanni biyu da kuma raayoyin wasu masana na yankin caribiyan da kuma Latin na Amurka na ganin cewa dalilin da isa kasar Amurka tayi uwa tayi makarbiya kann ganin an dauki wannan mataki na gudanar da kasuwanci a tsakanin kasashen ba tare da kace nace ba,madaface da zata dogara a kanta wajen fadada karfin mulkinta tare da juya akalar tattalin arzikin yankin baki daya,wanda hakan kuma ka iya jefa miliyoyin yan kasashen a cikin kaka ni kayi na fatara.
Bugu da kari ire iren wadan nan mutane na ganin cewa shugaba Bush na Amurka na,a matsayin mutumin daya taimaka wajen ganin kasashen sun dauki wannan mataki kann harkokin kasuwancin,duk kuwa da cewa akwai yarjejeniya da aka cimma na cewa da sauran lokaci kafin a yanke shawara ta karshe kann batun kasuwancin.
A yanzu haka dai wadan nan banbance banbance da aka samu a tsakanin kasar ta Amurka da kuma wasu kasashe na yankin na Latin Amurka na nan na sama yana kasa,duk kuwa da yarda da taron kolin yayi ga wasu batutuwa na daban a fannonin rayuwan bil adama daban daban.