1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda Sallar Azumin bana ta riski 'yan gudun hijira

June 23, 2017

Yayin da al'umar da ke zaune gidajensu ke shirye-shiryen Sallar Azumin bana, daruruwan 'yan gudu a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, za su yi tasu Sallar ne ba tare da wani bambanci da sauran ranaku ba.

https://p.dw.com/p/2fI9g
Eid Fest in Nigeria
Hoto: DW/A. A. Abdullahi

Duk da cewa ba a rasa wasu da suka kai tallafi ga wasu 'yan gudun hijirar domin su ma su yi kwatankwacin yadda sauran al'uma ke yi ba, ga alama 'yan hijiran za su yi bukin Sallar ne cikin yunwa da rashin tufafin adon wannan muhimmin biki.

A ziyarar da DW ta kai wasu sansanonin 'yan gudun hijira a sassan birnin Maiduguri na jihar Borno an tarar da 'yan gudun hijirar na rayuwar da suka saba, ta ba bu wani takamaimen shiri don zuwa Sallar karama wacce ke alamta karewar Azumin watan Ramadana. Wasu da ma da na tarar ba sa ma samun abinda za su yi bude baki da shi inda wadan ke da shi ke tsumulmular sa saboda ya kai su kareshen Azumin don kar su rasa abincin bude baki bayan kwashe yini su na Azumi.

Nigeria Frauen erzählen vor ihre Gefangenschaft bei Boko Haram
Hoto: Reuters

Ga wanda ya ke cikin wannan hali ba za a yi zaton zai iya tunanin yin wani shiri domin Sallah ba inda abin da ya fi tunani shi ne abin da zai kashe masa yunwar cikinsa. Mata da yara da galibi aka sani da dabbaka wannan biki, sun ce su dai babu wani bambancin ranar Sallar da sauran ranaku, saboda halin da su ke ciki.

Nigeria Flüchtlinge wegen der Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A wani mataki na karfafa dankon zumunci dage tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, wasu daga jamhuriyar Nijar sun kawo turamen atamfa domin tallafa wa 'yan zaman hijira a Maiduguri don su samu kayan Sallah. Wadannan bayin Allah sun raba daruruwan turamen atamfofin ga 'yan gudun hijira inda kuma suka bayyana cewa sun yi wannan tallafi a jihar Diffa da ke jamhuriyar Nijar. Sun nuna cewa ya kamata kowane bangare na al'uma su taimakawa wadannan bayin Allah ko da ba 'yan kasar su bane, ganin a halin da su ke ciki na neman taimako ko wane iri.

Masharhanta dai sun bayyana bukatar jama'a su tallafawa wadanda suka gamu da jarrabawa ta ra'ayuwa, ko za su samu sanyi a zukatansu.