Yadda kafofin sadarwan Amirka ke ba da labaran batanci. | Zamantakewa | DW | 08.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yadda kafofin sadarwan Amirka ke ba da labaran batanci.

An kiyasci cewa, yawan musulmin Amirka ya kai kusan miliyan biyu. Duk da cewa kafofin yada labaran kasar sun yi ta buga rahotanni daban-daban kan batancin da aka yi wa manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cikin wata jaridar kasar Denmark, jaridun Amirka kalilan ne suka yunkuri buga hotunan zanen da suka janyo bacin ran musulmi a duniya baki daya.

Ginin majalisar dattijan Amirka a birnin Washington

Ginin majalisar dattijan Amirka a birnin Washington

Daga cikin manyan gidajen talabijin na Amirka, tashar na ta ABC ce kawai ta nuna hotunan zanen batancin nan a cikin shirye-shiryenta. Wata kakakin tashar ta ce, an dau shawarar nuna hotunan ne don bai wa masu kallo da sauraro damar yanke wa kansu shawara, bayan sun san abin da ake korafi a kansa takamaimai.

Sauran tashoshi kamarsu NBC da CBS da kuma CNN, su ma sun yi ta ba da cikakkun labarai game yadda al’amura ke ta kara tabarbarewa a kan wannan batun, sai dai bas u nuna hotunan zanen ba. Kazalika kuma, kamfanin dillancin labaran nan AP, shi ma ya guji sayad da hotunan zanen ga gidajen buga jaridu. Mafi yawan jaridun Amirkan, su ma sun ki buga hotunan zanen. kalilan daga cikinsu ne, kamar dai jaridar nan „Philadelphia Inquirer“, suka yunkuri daukar kasadar buga hotunan a shafunansu. Kai tsaye ne dai kuma, musulmin birnin na Philadelphia suka yi jerin gwano zuwa ma’aikatar buga jaridar don bayyana bacin ransu da buga hotunan zanen batanci ga annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da ta yi. Babbar editar jaridar, Amanda Bennett, ta yi kokarin kwantar musu da hankali da cewa:-

„Ina tabbatar muku cewa, da ni da wannan jaridar, ba mu da wata sha’awar nuna muku ko kuma addininku duk wani irin wulakanci. Ina son kuma ku san cewa, ina alfaharin ganin yadda kuka yi amfani da `yancin bayyana ra’ayoyinku na bacin rai gaban wannan ginin.“

A cikin hotunan zanen da jaridar ta Philadelphia Inquirer ta buga dai, har da wanda ke siffanta annabi Muhammadu, salallahu alaihi wassalam, da rawani mai kunshe da nakiya, wato abin ke kwatanta shi da `yan ta’adda. Sai dai, ba a farkon shafinta ne ta buga hotunan ba. A fakaice ta buga su, da wani dan bayani kan inda za a iya gano su a tsakiyar jaridar. Ko me ya sa suka yi haka ? Babbar editan jaridar, Bennett, ta bayyana dalilinsu ne da cewa:-

„Muna ganin dai wannan batun na da muhimmmanci kwarai, sabili da haka ne muke son bayyana wa masu karantunmu abin da ya kunsa. Hoton da kansa kuwa na da nasa ma’anar.“

A ma’aikatar buga jaridar Boston Globe kuwa, sai da editoci suka shafe tsawon lokaci suna ta muhawara kan buga hotunan ko kuma a’a. A karshe dai masu adawa da buga su ne suka fi rinjayi, kuma a kan hakan aka tsaya, inji cif editan jaridar, Marty Baron. Ya kara da cewa:-

„Sau da yawa dai, muna samun hotuna, wadanda ke nuna wulakanci ga wani rukuni na al’umma ko kuma na addini. To manufar buga jaridarmu dai ita ce: kaucewa daga buga wadannan hotunan.“

Irin wannan manufar ne dai kuma jaridun „Washington Post“ da „New York Times“ ke bi. Amma daya jaridar ta birnin New York, wato „New York Sun“, ita ma ta buga hotunan zane biyu daga jerin 12 da jaridar Denmark ta fara bugawa. A shafin yanar gizo ta gidan rediyon NPR, wadda ita kadai ce ba ta tallce-tallace a shirin da take yadawa a duk fadin kasar, an nemi hotunan zanen an rasa, abin da ke nuna cewa, a daura da yadda za a yi zato ko hasashe, kafofin yada labaran Amirka kalilan ne, wadanda suka wuce gona da iri wajen yayata hotunan zanen batancin.