1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda al'umman Iran ke ganin rikicin da ake yi da kasarsu game da batun makamashin nukiliyanta.

February 2, 2006

Yayin da ake ta ka ce na ce a taron Hukumar Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa a birnin Vienna, game da rikicin da ake yi da kasar Iran kan batun makamashin nukiliyanta, `yan kasar da kansu ba sa nuna wata fargaba ko damuwa game da barazanar sanya musu takunkumi ko ma afka musu da yaki.

https://p.dw.com/p/BvTu
`Yan kasar Iran, a zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatinsu a kan batun makamashin nukiliya.
`Yan kasar Iran, a zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatinsu a kan batun makamashin nukiliya.Hoto: AP

A kasar Iran dai ranar alhamis ce jajiberen karshen mako, kamar yadda ranar juma’a take a wasu kasashen da ba na musulmi ba. Sabili da haka, mafi yawan al’umman kasar na begen hutawa ne daga hayaniyar makon, maimakon su mai da hankalinsu ga al’amuran siyasa. Akwai ababan da ke damunsu, wadanda kuma ke jan hankullansu, fiye da bata lokaci kan wai wata hukumar makamashin nukliya da ke can nesa a birnin Vienna, kai ko ma a kan wani kwamitin sulhu da ke birnin New York, wanda daga gare su ke can wata duniya fiye da Viennan ma nisa. Al’umman Iran din dai, ba sa nuna alamun tsorata ko kuma damuwa ga barazanar da ake yi wa kasarsu. A nasu ganin, babu wata ja da baya, daga manufofin makamashin nukilyan da Jumhuriyar Islaman ta sanya a gaba.

Mazauna birnin Teheran dai na bayyana ra’ayoyi daban-daban a kan wannan batun. Amma dukkansu kuma na goyon bayan shirin da gwamnatin kasar ta tsara na mallakar wannan fasahar ta samar wa kanta da kanta makamashin nukiliya. Malama Atoussa, wata mace ce mai sassaucin ra’ayi, wadda ke aiki a wani kamfanin talla a birnin na Teheran. A nata ganin dai:-

„Mallakar fasahar makamashin nukiliya, wata fa’ida ce ga kasarmu. Bai kamata kuma mu ki daraja hakan ba. Iran kasa ta ce, ina farin ciki da kasancewa `yarta, kuma ina begen ganin cewa ta kasance kakkarfar kasa.“

Kusan duk `yan kasar Iran din dai na alfahari da kasarsu. A halin yanzu kam, wannan batun makamshin nukilyan ya hade kawunansu a wuri daya, inda kuma suke nuna cikakken goyon bayansu ga manufofin gwamnatin kasar. Kamar yadda wani mutum a kan titin birnin Teheran ya bayyanar:-

„Ina matukar farin cikin kasancewa dan kasar Iran. Kuma ko wane ba Irane na alfahari da wannan kasar, musamman idan ya fahimci cewa kasarsa ma ta mallaki wannan fasahar.“

Kazalika kuma wata mace a dai wannan gun, ta bayyana ra’ayinta ne kamar haka:-

„Tabarakallah ! Yannzu dai kasata ma, ta kai matsayin da sai an dama da ita a harkokin duniya.“

Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad dai, na sane da wannan goyon bayan da yake sammu daga al’umman kasarsa a kan wannan batun. Rikicin da ya barke tsakanin kasarsa da kasashen Yamma a kan wannan batun na makamshinm nukiliya dai, ya janyo masa wata fa’ida ta hade kan duk jama’an kasar wajen nuna masa wannan goyon baya. A wani taron gangami da aka shirya masa a garin tashar jirgin ruwa na Bushehr jiya, ya bayyana cewa:-

„Wannan kira da jama’an garin Bushehr ke yi yau, shi ne kuma kiran da sauran duk `yan kasar Iran ke yi. Wato makamashin nukilya dai, hakkinmu ne, wanda kuma ba za mu taba sayad da shi ba.“

Shugabannin addinin kasar dai, sun sha nanata cewa, ba su da burin mallakar bam na nukiliya. Hakan ya saba wa addinin islama. Wani gungu na `yan zanga-zanga a birnin Teheran ma sun yi ta shelanta hakan cikin turanci, don a fahince su a ko’ina, ko da a Amirka ne ma:-

„Na’am ga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukilya – Assha ga makaman kare dangi.“

Mafi yawan `yan kasar Iran din, a zahiri, ba sa fargabar wani takunkumin da ake barazanar sanya musu. Da farko dai galibi daga cikinsu, na bayyana alfaharinsu ne da kasarsu. Na biyu kuma, ba su yarda da kasashen Yamma ba. A takaice dai, wani dan kasar ya bayyana ra’ayinsa game da barazanar da kasashen Yamman ke yi wa Iran ne kamar haka:-

„Inganta sinadarin Yureniyum, wani hakki ne na tsantsa da Iran ke da shi, kuma babu wanda ya isa ya hana mu tafiyad da wannan aikin. Idan Amirka ta yi barazanar afka mana da yaki, farashin man fetur zai tashi kai tsaye ne a kalla zuwa dola 100. Saboda hakan ma kawai, ba za su iya hana mu ci gaba da wannan aikin ba ko kuma su yunkuri afka mana da yaki. Ko da sun yi hakan ma, zai kasance aikin banza ne kawai.“