Yaa Nana Asantewaa -Jarumar sarauniya | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 17.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Yaa Nana Asantewaa -Jarumar sarauniya

Yaa Nana Asantewaa ta yi fice a kan rawar da ta taka a fage na jarumta a yakin kujerar gwal (Golden Stool), mace ce mai jajircewa. A baki dayan rayuwarta ta yi kokari wajen kare daularta.

DW Videostill Projekt African Roots | Yaa Asantewaa, Ghana (Comic Republic)

Yaa Asantewaa: Jarumar Sarauniya

Ta rayu tsakanin shekarar 1840 a (Besease, daular Ashanti) zuwa 17 ga watan Oktoba 1921 a (Seychelles)

Abin da ya sa ta yi fice: Ta zaburar tare da ba da taimako ga abin da a yau a ke kira da yakin kujerar gwal. Wannan kujerar yaki har yanzu na zama abin alfahari ga al'ummar Ashanti, wakilin Birtaniya a wancan lokacin, Sir Frederick Mitchell Hodgson ya nemi a ba shi wannan kujera ya zauna a madadin sarauniyar Ingila.

Ta mayar da martani ga mazajen Ashanti dangane da bukatar wakilin Birtaniya tana mai cewa:

"[…]Da gaske ne jarumtakar al'ummar Ashanti ta gushe? "Na yi mamaki matuka, ba zai yi wu ba, na tilas in bayyana hakan! Idan ku mazan Ashanti ba zaku ja gaba ba, mu zamu iya , zan kira 'yan uwana mata mu yaki wadannan Turawa. Zamu yi yaki har sai dayanmu da ya yi saura ya fadi a fagen daga. Idan ku shugabanni ba zaku iya fada ba zamu sauya sutrura ku karbi tawa na karbi taku."

- Kasancewar ta wadda sarakunan Ashanti suka sanya ta jagorancin yaki, ta kasance mace ta farko kana guda daya tilo da ta kasance ja gaba a filin daga da bayar da shawarwari da sabunta kayan yaki ga sojojin Ashanti a yayin da take da shekaru 60 a duniya!

A dubi bidiyo 01:59

Tarihin Yaa Nana Asantewaa

Abin da ta bari: Yaa Asantewa babbar abar koyi da alfahari ce a wajen yara mata da manyan mata a kasar Ghana da ma kasashen Afirka baki daya. Mata da dama da suka yi fice wajen nuna kwarewa a fagen da maza ke da rinjaye, akan musu lakabni da Yaa Asantewaa a wani mataki na bada karfin gwiwa da goyon baya.

In 2000, a museum was dedicated to the memory of the great warrior queen in Ejisu. Her family was generous enough to contribute heirlooms and articles that Yaa Asantewaa actually used, including items of clothing as well as a turtle shell in which she was said to have eaten her meals. Unfortunately, the museum was gutted by fire in July 2004. Most of the things were lost and the museum still stands in ruins.

 A shekarar 2000 an sadaukar da wani gidan tarihi don tunawa da wannan sarauniya a fagen yaki a Ejisu. Iyalanta sun taimaka kwarai wajen bayar da kayan da suka gada a wajenta da ma wadanda ta yi amfani da su lokacin da take raye da suka hadar da sutturu da kwanikan da aka ce a cikinsu take cin abinci. Sai dai abin takaici a watan Yuli na shekara ta 2004, gidan tarihin ya kama da wuta, inda gobarar ta lakume kayan cikinsa masu yawa, kana har yanzu ba a gyara shi ba.

An sanya sunanta ga makarantar sakandaren gwamnati ta farko a Kumasi, wato "Yaa Asantewaa Senior Girls' High School."

 

Pinado Abdu-Waba da Ramatu Mahmud Abubakar Jawando da Gwendolin Hilse ne su suka yi hidima wajen haduwar wannan labari. Shiri na musamman na bitar tarihin Afirka, da zai rika zuwa kashi-kashi "African Roots", shirin hadin gwiwa da cibiyar Gerda Henkel.

 

 

 

 

 

 


 

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin