1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ya kamata kasashen musulmi su kalubalanci na yamma

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad yayi kira ga kasashen musulmi da su yi amfani da karfin tattalin arzikinsu don tinkarar duk wani kalubale daga kasashen yamma. A jawabin da yayi a karshen ziyarar da ya kaiwa Syria shugaba Nijad ya ce kasashen musulmin ke da laifi idan suka taimakawa tattalin arzikin kasashen yamma. Shugaban ya ce ta haka suna ba wa´yan yamma damar yin amfani da karfi akan su. A dangane da takaddamar shirin nukiliyar kasar kuwa, ´yan siyasa a birnin Teheran sun yi gargadi game da wani sabon rikici a fannin samar da mai. A kuma halin da ake ciki mujallar Spiegel ta nan Jamus ta rawaito cewar hukumomin Iran sun gabatarwa ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier wata sabuwar shawarar game da warware rikicin nukiliyar.