Yaƙin neman zaɓe a ƙasar Tchad | Labarai | DW | 02.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙin neman zaɓe a ƙasar Tchad

Yau ne, a ƙasar Tchadi, a ka buɗa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, da za a yi ranar 3 ga wata mai kamawa.

Shugaba mai ci yanzu, Idriss Deby Atno, ko shakka babu, za shi tazarce, karro na 3, dalili da shawara da manyan jam´iyun adawa su ka yanke, ta ƙauracewa zaɓen.

Idriss Deby, ya yau karagar mulkin tchadi , ta hanyar juyin mulki,yau shekaru 16 da su ka gabata.

Ya ajje takara, tare da sauran yan takaran jeka na yi ka, na wasu ƙanana jam´iyu guda 4, da su ka haɗa da tsofan Praminsita Kassire Coumakoy, na jam´iyar Viva RNDP, da ministan harakokin noma mai ci yanzu, Pahimi Padacke, na jam´iyar RNDT, da ministan kulla da passalin jihohi da ƙananan hukumomi, Mahamat Abdullahi na jam´iyar MPDT, sai kuma Brahim Koulamallah, daga jam´iyar MSA.

Yan adawar ƙasar Tchadi, sun gwamace, ƙin shiga zaɓen bayan sun binciko, mattakan maguɗi da gwamnati ta tsara.

Sun gitta sharruɗan, rushe tsarin zaɓen gaba ɗaya, da kuma hawa tebrin shawara, domin shinfiɗa sabin matakai, da za su samu karɓuwa, daga ɓangarori daban-daban na siyasa.

Wannan yaƙin neman zaɓe na wakana, a yayin da shugaba Idriss Deby, ke fuskantar ƙalu bale, daga kungiyoyin tawaye, da a yanzu haka, ke ci gaba da gwabzawa ,da dakarun gwamnati, a gabacin wannan ƙasa.