Yaƙin neman zaɓe a ƙasar kamaru | Labarai | DW | 17.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙin neman zaɓe a ƙasar kamaru

Madugun yan adawar ƙasar Kamaru John Fru Ndi, ya zargi shugaba Paul Bia, da kitsa maguɗi a zaɓen yan majalisun dokoki da nana kansiloli wanda za a shirya a ƙasar ranar 22 ga watan da mu ke ciki.

Shugaban jam´iyar SDF mai adawa, da ya zo na 2 a zaɓen shugaban ƙasar shekara ta 2004, ya bayyana saban matakin yanke -yanke johohi da ƙananan hukumomi ,a matsayin wani salo na aringinzon ƙuri´u, da jam´iyar RDPC mai riƙe da ragamar mulki ta shirya, da zumar samun gagaramin rinjaye a majalisar dokoki.

Burin ƙarshe da su ke buƙatar cimma ,shine gudanar da kwaskwarima ga kudin tsarin mulki, domin baiwa shugaba Paul Biya, damar sake ajje takara, a zaɓen shekara ta 2011.

Shugaban ƙasar Kamaru ya hau kujera mulki tun shekara ta 1982, wato shekaru 25 kenan da su ka gabata.

Cemma, a wani taro da su ka shirya, a ƙarshen mako, ƙungiyoyin kiristocin Kamaru, sun zargi shugaban majalisar dokokin ƙasar, da kitsa maguɗi, bayan ya alƙawarta jika ɗari na CFA, ga dukkan mazaɓun da jam´iyar sa, ta lashe zaɓen.