Yaƙin Libanon | Labarai | DW | 09.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙin Libanon

Rundunar ƙasar Libanon ta ƙara asara sojoji 3, a gumurzun da ta yi yau, da yan takifen Fatah Al-Islma, a yankin Nahr Al Bared.

A baki ɗaya mutane 108 su ka rasa rayuka, daga farkon yaƙin, ranar 20 ga watan mayu, zuwa yanzu.

Shehhunnan mallumai, na ƙasashen Libanon da Palestinu, sun girka komitin shiga tsakani ,domin sasanta wannan rikici.

Membobin wannan komiti, sun yi ganawar farko da kakakin Fatah Al Islam Chahine, Chahine.

Nan gaba a yau, za su sadu da shugaban rundunar Libanon Jannar Michel Sulaimane.

Ƙungiyar Fatah Al-Islam ta yi barazanar faɗada yaƙin ga sauran sassan Libanon, muddun sojojin gwamnati, basu dakatar da kai hare-haren kann mai uwa da wabi ba, a yankin Nahr Al Bared.

Ƙungiyoyin bada agaji, sun bayyana zullumi, a game da tsamarin da faɗan ya yi, abunda ke hadasa matsaloli ta fannin kai taimakon abinci da sauran kayan more rayuwa, ga yan gudun jijira da ke zaune a yankin Nahr Al Bared.