Yaƙin Afghanistan | Labarai | DW | 04.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙin Afghanistan

A Afghanistan, yan ƙunar baƙin wake, sun kai wani saban hari ga dakarun ƙungiyar tsaro ta NATO, ko kuma OTAN dake birnin Khandahar a kuduncin ƙasar.

Saidai bai samu sa´ar cimma buri ba.

Wannan hari ya kasance tamkar martani, ga mutuwar wani jigo a ƙungiyar Taliban a yankin Musa Qala, da yan taliban ɗin su ka ambata capkewa ranar juma´a da ta wuce.

Rahotani daga yankin su ce, run dunar NATO ta matsa ƙaimi wajen kai hari a yanki na Musa Qala, wanda a sakamakon hakan, al´umma ke ci gabada ƙaurace masa.

Gwamnatin Afghanistan tare da tallafin rundunar ISAF, ta watsa takardu, inda su ka gayyaci yan taliban su gaggauta fita daga yankin , idan kuma su ka ƙi, to jiki magayi.