Yaƙi ya sake ɓarkewa a Libanon | Labarai | DW | 29.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙi ya sake ɓarkewa a Libanon

Saban rikici ya ɓarke a ƙasar Libanon, tsakanin dakarun gwamnati da ƙungiyar sa kai, ta Fatah al Islam.

Rundunar gwamnati Libanon, da ta samu nasara a kann yan takifen,a kwanakin baya ta ja daga, a kewayen sansanin yan gudun hijira na Nahr al-Bared.

Shugaban ƙasar Libanon Emil Lahud, da a ke ɗauka tamkar ɗan amshin shatan Syria, ya gabatar da shawarwari na fita daga wannan ƙangi.

Lahud ,ya bukaci girka gwamnatin haɗin kann ƙasa, wanda zai duƙufa wajen ayyukan maido da zaman lahia, da kuma warware rikicin siyasa da Libanon ke fuskanta.

Saidai ba da wata-wata ba, masu adawa da Emil Lahud, sun yi wasti da wannan shawara.