Yaƙi ya ɓarke a Libanon. | Labarai | DW | 22.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙi ya ɓarke a Libanon.

A arewancin ƙasar Libanon, an shiga rana ta 3, a na gwabza faɗa, tsakanin dakarun gwamnati, da ƙungiyar Fatah Al -Islma.

Wannan rikici da ya ɓarke tun ranar lahadi da ta gabata, ya hadasa mutuwar mutane kimanin 60 ya zuwa yanzu.

Ƙungiyar Fatah Al-Islam, ta ƙunshi Palestinwa masu tsautsaran ra´ayin addinin Islama, da su ka samu mafaka a ƙasar Libanon, wanda kuma mafi yawan su ke zaune a matsugunin Nahr Al Bared.

Rundunar ƙasar Libanon

a jiya litinin, ta yi ruwan harssasai a wannan yanki, wanda a sanadiyar sa, mutane fiye da 40 su ka kwanta dama.

Ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa sun yi kira ga ɓangorin 2, su tsagaita wuta, domin ceton fara hulla da yaƙin ya rutsa da su.

Ƙasar Syria, ta hito hili, ta ƙaryata zargin da ake mata, na bada taimako ga ƙungiyar Fatah Al-Islam.

Wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia a ƙasar Libanon, Terje Roed-Larsen, ya kira da babbar murya ga, ƙasashen dunia, su gaggauta sa hannu, domin kawo ƙarshen wannan saban rikici a ƙasar Libanon.