Yaƙi tsakanin Isra´ila da Hezbollah | Labarai | DW | 17.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙi tsakanin Isra´ila da Hezbollah

A na ci gaba da ɓarin wuta tsakanin dakarun Isra´ila da na Hezballah.

Rundunar Isra´ila na amen bama bamai ta sararin samaniyar birnin Beyruth da kudancin Labanon, wanda a sakamakon zu kussan mutane 200 su ka rasa rayuka.

A nasu ɓangare dakarun Hezbollah sun ƙara harba rokoki a yankunan Saint Jean d´Acre, Nahariya da Haifa dukan su a arewancin Isra´ila.

A yayin da ya yi jawabi jiya, ta kafofin sadarwa shugaban Hezbolah Hassan Nasrallah, ya tabatar da cewa, za su ci gaba da kai hare hare muddun Isra´ila, ba ta amince ba, a yi masanyar Pirsinoni, da sojojin ta guda 2, da ke cikin hannun Hezbollah.

Ta la´akari da yadda rikicin ya ƙara ƙamari ƙasashen turai da Amurika, na ci gaba da kwashe al´ummomin su da ke zaune a ƙasar Labanon.

A lokacin da ya gabatar da jawabi a taron ƙasashe mafi ƙarfin tattalin arziki a dunia, Praministan Britania Tony Blair, ya bayana hanyyonin shawo kan wannan rikici.