Yaƙi da ta´adda a Jamus | Zamantakewa | DW | 16.09.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yaƙi da ta´adda a Jamus

Daga cikin matakan kandagarkin hare haren ta´addanci har da tare saƙonnin email da sauraron hirarraki ta wayar tarho. Sai dai hakan na janyo kace-nace tsakanin ´yan siyasa a nan Jamus.

default

Ministan cikin gida Wolfgang Schäuble

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na Duniya Mai Yayi. To a yau dai shirin yana nan gida ne wato Jamus, inda ake ci-gaba da kace-nace kann matakan gwamnati na bin diddigin saƙonnin email da sauraron hirarrakin jama´a ta wayar tarho a cikin matakan ta na yaƙi da ta´addanci. Shin wannan matakin na tasiri kuwa. Shin ba a wuce gona da iri a wannan matakan da gwamnati ta ce na kandagarki ne don hana kaiwa ƙasar wani harin ta´addanci shigen wanda aka kaiwa Amirka a ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001? Muna ɗauke da ƙarin bayani a cikin shirin.

Shekaru bakwai da suka wuce wato a ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001, duniya ta kaɗu sakamakon hare haren ta´addanci da ke zaman irinsa mafi muni gabanin wannan lokaci. Hare haren a biranen New York da Washington na ƙasar Amirka sun yi sanadiyar mutuwar dubban mutane. A dangane da haka an tsaurara dokokin tsaro. Ko da yake kawo yanzu tarayyar Jamus ba ta fuskanci irin wannan hari ba, amma duk da haka ofishin ´yan sanda ciki na tarayyar na mai ra´ayin cewa ´yan tarzoman musulmi sun ƙuduri aniyar kai sabbin hare hare a wasu ƙasashe ciki har da a nan Jamus.


B. Ra´ayoyi sun banbanta kan yadda za a tsara matakan tsaro a nan Jamus. Kakakin ɓangaren jam´iyar social democats a majalisar dokoki ta Bundestag kuma masani kan harkokin siyasa na cikin gida, Dieter Wiefels-Pütz ya yi nuni da cewa mazauna a birnin Berlin fadar gwamnatin tarayya sun fi takwarorinsu a biranen London da New York samun cikakken tsaro na rayuwa. Wannan iƙirari na ɗan majalisar na da ƙanshi gaskiya domin kawo yanzu ba a kaiwa babban birnin na Jamus ko ma ƙasar baki ɗaya wani mummunan hari ba.


To sai dai duk da haka masana na hukumomin leƙen asiri da na ofishin ´yan sanda ciki na tarayya na gargaɗi da yin sako-sako. Su ce tuni Jamus ta shiga taskar musulmi ´yan tarzoma. Kimanin shekara guda da ta wuce ƙiris ya rage a kaiwa ƙasar hari. Domin a yankin Sauerland jami´an leƙen asiri sun yi nasarar bankaɗo tare da kame wasu mutane da ke shirin kai hare hare bam da motoci akan cibiyoyi da sansanonin Amirka da ke cikin ƙasar ta Jamus. A dangane da wannan nasara da jami´an binicke suka samu, ministan harkokin cikin gida Wolfgang Schäuble ya ce haka tabbaci ne ga matakan sa na bawa hukumomin tsaro ƙarin iko.


1. Schaüble

„Wannan abin ya kasance babban hatsari ga ƙasarmu da al´ummarta gaba ɗaya. Wani hatsari ne da aka hana shi aukuwa. Yanzu muna magana ne game da wata barazana ta zahiri. Muna da ´yancin zama cikin wata ƙasa mai cikakken tsaro, saboda haka ya zama wajibi mu bawa hukumomin tsaron mu dukkan goyon baya da suke buƙata don tafiyar da aikinsu na kare ƙasa da jama´ar dake cikinta.“


Tun bayan hare haren 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 a Amirka, an tsauraran dokoki a nan Jamus. Alal milsali bayan an janye wata gatar tafiyar da addini, hukumomin tarayyar Jamus sun haramta ayyukan ƙungiyoyin addinin musulunci da dama waɗanda ake zargi da zama wata matattarar masu iya kai harin ta´addanci. Sannan an bawa masu shigar da ƙara da hukumomin tabbatar da bin doka da oda ƙarin ikon gudanar da bincike kan matafiya musamman ta jiragen sama, hanyoyin sadarwar da takardun ajiyar bankin na ɗaiɗaikun mutane. Yayin da aka sanya wasu abubuwan na halittar mutum a cikin takardunsa na shaida.


B. Masu kare bayanai na jama´a da jam´iyun siyasa na wannan ƙasa sun yi watsi da wannan matakin da cewa katsalanda ne cikin harkokin yau da kullum da kuma ´yancin walwala na jama´a. Suka ce abin da gwamnati ta sa gaba shi ne bawa hukumomin leƙen asiri izinin gudanar da binciken cikin sirri ta amfani da wasu abubuwa dale janyo tutsun nau´rar komputa. Masanin harkokin siyayar cikin gida na jam´iyar The Greens Wolfgang Wieland ya ce gwamnati ta na son ta yiwa majalisar dokoki ɗan waken zagaye ne dangane da ´yancin ta na gudanar da bincike.


2. Wieland:

„Za mu samu wani sabon ofishin ´yan sandan ciki na tarayya, wanda zai iya yin dukkan wani aiki da ofishin tarayya dake kare kundin tsarin mulki ke yi, amma ba tare da majalisa ta samu damar gudanar da bincike kan su ba.“


Ita ma mai magana da yawun jam´iyar ´yan ra´ayin gurguzu akan harkokin siyasar cikin gida Ulla Jelpke cewa ta yi ba bu banbanci tsakanin sabon ofishin ´yan sandan ciki da hukumar leƙen asiri ta ´yan sanda a zamanin mulkin ´yan NAZI.


3. Jelpke:

„Abin da aka yi ba komai ba ne illa ƙirƙiro wata rundunar ´yan sandan leƙen asiri musamman a kan rayuwar yau da kullum ta jama´ar wannan ƙasa. Wannan wani abin kunya ne da ba ma bukatarsa ko kaɗan a wannan ƙasa.“


Kalaman da Jelpke ta yi amfani da su na nuni da yadda muhawwara game da sha´anin tsaron ta yi zafi a nan Jamus. Ko da yake shi ma muƙaddashin shugaban ɓangaren jam´iyun haɗin guiwa na CDU da CSU a majalisar dokoki Wolfgang Bosbach ya amsa cewa ba wanda zai iya ba da tabbacin tsaro 100 bisa 100, amma ya ce yana goyon bayan tsaurara dokokin tsaro.


4. Bosbach

„Kawo yanzu mun bankaɗo shirin kai mana hare hare har bakwai a nan Jamus. Allah ne kaɗai Ya tona asirin waɗanda suka shirya kai waɗannan hare haren tun ba su yi nisa ba. Ba nasarar binciken ´yan sandan ciki ta hana kai hare haren nan da wasu akwatuna da aka cika su da bama-bamai shekaru biyu da suka wuce ba. Rashin ƙwarewar waɗanda suka shirya kai harin ne. Godiya ta tabbata ga Allah da bai ba su wannan ƙwarewa ba.“