1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙi da cutar ƙanjamau

Babban bankin duniya yace yaƙi da kwayar cutar ƙanjamau HIV zai yi nasara ne kawai idan ƙasashe masu haɗarin cutar suka himmatu wajen daƙile yaɗuwar ta. Julian Schweitzer ta reshen bankin duniyar a kudancin Asia, ta ce ya kamata ƙasashen su mayar da hankali wajen matakan hana yaɗuwar cutar, maimakon kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen magani ga mutane ƙalilan da suka kamu da cutar. Jamiár ta baiyana hakan ne a wajen babban taro na duniya kan cutar ƙanjamau wanda ke gudana a yanzu haka a birnin Toronto na ƙasar Kanada. Bayanai sun nuna cewa daga cikin adadin mutane miliyan 65 waɗanda suka kamu da ƙanjamau a duniya, cutar ta kashe mutane miliyan 25 ya zuwa yanzu. Cutar ta Kanjamau ta fi ƙamari a ƙasashen Afrika da kuma kudancin Asia.