Yaƙi a Sri Lanka | Siyasa | DW | 07.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaƙi a Sri Lanka

Yan tawayen tamoul Tigers da dakarun gwamnatin Sri Lanka na ci gaba da ɓarin wuta.

default

Al´ummomin Sri-lanka sun shiga cikin wani halin ruɗani a sakamakon ƙara ƙamarin ɓarin wuta tsakanin yan tawayen Tamoul Tigers da dakarun gwamnati.

A tsukin yan kawanaki 2, hare hare tsakanin ɓangarorin 2 ya hadasa mutuwar mutane masu tarin yawa.

Tun shekara ta 1972 a ka fara gwabzawa wannan rikici wanda ya zuwa yanzu ya jaho assara rayuka fiye da dubu 60.

Ranar lahadi da ta wuce yan tawayen Tamoul -Tigers a ranar lahadin da ta gabata su zargi gwamnati ta saɓa alƙawuran da ta ɗauka na tsaigata, a sakamakon yarjenejeniyar da su ka rattaba hannu a kan ta, a shekara ta 2002.

A game da haka ,yan tawaye su ka su kai farmaki a wurare da dama.

Gwamnatin Sri Lanka, ta yi watsi da tayin yan tawayen na hita daga magudanar ruwa, ta Maavilaru da su ka datse.

A cikin wannan yanayi ne,na tashe tashen hankulla wasu ma´aikatan ƙungiyar bada agaji ta ƙasar France“ Action contre la Fin „ su 16 su ka gami da ajali a Muttur, yanki da ya fama da rikicin.

Ya zuwa yanzu, babu wani cikkaken bayyani a game da yada wannan jami´ai su ka rasa rayuka, da kuma wanda su ka hallaka su.

Ɗaya daga magabatan ƙungiyar, Andrew Mitchell ya sanar manema labarai cewa, za su dakatar da dukan ayyuka na wucin gadi a ƙasar Sri Lanka:“Abun da mu ka yi shine, dakatar da ayyukan mu, har sai mun samu cikkaken bayyanai akan mutanen da ke da alhakin aikata wannan kissa, mu kuma samu dalilan da ya sa su aikata hakan“.

Bayan mu samu wannan bayani, za mu gudanar da tunani a kan haɗarurukan da mu ke tare da su, da kuma hanyoyin da ya kamata zuwa gaba mu gudanar da ayyukan.

Ƙasashe da ƙungiyoyin daban-daban, na dunia, na ci gaba da Allah wadai da wannan kisa.

Shugaban tawagar sa ido a kan tsagaitar wuta tsakanin yan tawaye da gwamnatin Sri-Lanka, Ulf Henricsson, ya danganta wannan ɗayan aiki, da mayar da hannun agogo baya, ga yunƙurin da ake, na samar da zaman lahia mai ɗorewa.

A Sri-lanka ana ci gaba da masanyar wuta, tsakanin yan tawayen Tamoul Tigers da dakarun gwamnati.

 • Kwanan wata 07.08.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btyl
 • Kwanan wata 07.08.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btyl