1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙin neman zaɓe a France

April 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuN0

Yan takara a zagaye na 2, na zaɓen shugaban ƙasar France, na ci gabada yaƙin neman zaɓe.

A halin da ake ciki, tunni, yan takarar jam´iyar PS Segolene Royal, ta sami goyan baya daga sauran yan takara 8, masu aƙidar gurguzu,wanda basu kai labari ba, a zagaye na farko.

Nicolas Sarkozy da Segolene Royale sun shiga zawarcin ɗan takara jam´iyar UDF Fransois Bayrou, wanda ya sami kashi kussan19 bisa ɗari, na yawan ƙuri´un da aka jefa.

Segolene Royale ce, ta fara kira ga Bayrou, zuwa tantanawa da zumar cimma sakamakon haɗa ƙarfi a zagaye na 2.

Manazarta al´ ammuran siyasa a France, na kyauattata zaton cewar,akwai alamun cimma wannan manufa, to saidai babu tabbas indan magoya bayan sa za su amince.

A wani jawabi da yayi Nicolas Sarkozy, ya gitta wasu sharuɗa kamin ƙulla duk wani ƙawance.