Yaƙi a birnin Mogadiscio na Somalia
March 25, 2006Talla
A birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia, a na ci gaba da ɓarin wuta, tsakanin gungu 2, masu gaba da juna.
Tun ranar laraba da ta gabata, a ka fara wannan ɗauki ba daɗi, wanda a halin yanzu ya hadasa mutuwar mutane kussan 100.
Rahotani daga ƙasar, sun bayyana cewar a jiya juma´a, mutane 30 su ka rasa rayuka.
A halin da ake ciki, mazamna birnin sun fara shiga gudun hijira.
Tun bayan yaƙe yaƙen farko , jim kaɗan bayan kiffar ga gwamnatin shugaba Mohamed Siad Barre, a shekara ta 1991, wannan shine tashin hankali na farko irin sa, da ya ɓarke a birnin Mogadiscio.