Yƙin neman zaɓe a France | Labarai | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yƙin neman zaɓe a France

Dan jama´iyar jama´iyar UDF da ya zo sahu na 3,a zaɓen shugaban ƙasar France ya kiri taron manema labarai, a yau laraba.

Tun bayan bayyana sakamakon zaɓen, yan takara 2 da za su fafata zagaye na 2, su ka shiga zawarci jam´iyar UDF.

To saidai wannan jama´iya, ta yanke shawara ba magoya bayan ta, damar kowa ya zaɓi ɗan takara da ya fi dacewa da shi a zagaye na 2.

Fransois Bayrou, ya gayyace mutane kussan milion 7 da su ka kaƙa masa ƙuri´a a zagaye na farko, kowa ya yanke wa kansa shawara, ya kuma zaɓi wanda ya fi kwanta masa, tsakanin Nikolas Sarkozy ko Segolene Royal.

Saidai ya bukaci magoya bayan nasa, su kwan cikin shirin tunkara zaɓen yan majalisun dokoki, da za a gudanar a watan juni mai zuwa.

A game da ra´ayin kan sa, kalamomin da su ka hitto daga bakin Fransois Bayrou,na nuni ƙarrara, zuciyar sa ta fi karkata wajen Segolene Royal.

A cikin wannan taron manema labarai, ya zargi Nikolas Sarkozy ,da nuna alamomin shinfiɗa mulkin kama karya a France, indan har ya samu sa´ar lashe zaɓen ranar 6 ga wata mai kamawa.