1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wutar daji na ci-gaba da addabar ƙasar Girika

August 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuD8
Har yanzu ba´a shawo kan wutar dajin nan dake ci-gaba da addabar kasar Girika ba. Rahotannin na nuni da cewa kawo yanzu ma´aikatan kashe gobara sun kasa kashe wannan wutar daji wadda aka yi kiyasin cewa ta yi sanadiyaar mutuwar akalla mutane 50. Hukumomi a kasar ta Girika na fargaba game da rayukan daruruwan mazauna kauyukan kudancin kasar wadanda wutar ta yiwa kawanya. FM Kostas Karamanlis ya kafa dokar ta baci yana mai saka ayar tambaya game da tashin gobarar yana mai cewa wasu ne suka cunnata da gangan. Kawo yanzu ´yan sanda sun kame mutane 3 wadanda ake zargi da hannu a cunna wutar dajin. Kawayen Girika na KTT wato Faransa da Italiya da Sweden da kuma Jamus sun aika mata da jiragen saman kashe gobara.