Wutar daji na ci gaba a California | Labarai | DW | 22.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wutar daji na ci gaba a California

Akalla iyalai 25,000 aka kwashe su daga kudancin California a kasar Amurka yayinda gobarar daji ke ci gaba da ruruwa a yankin.Mutum guda ya rasa ransa a kusa da San Diego inda wutar taci kimanin hecta 14,000 daga yankin na San Diego zuwa arewacin santa Barbara.wasu jamian kashe gobara 4 da fararen hula 10 sun samu raunuka.Gwamnan jihar California Arnold Schwarzenegger ya aiyana dokar ta baci a yankuna 7 da gobarar tafi shafa.An kaddamar da bincike game da musabbanin gobarar sai kuma hukumonin kasar sun baiyana cewa akwai yiwuwar cewa wani layi na na wutar lantarki da ya fado ya haddasa ta.