Wulff a ƙasar Turkiya | Labarai | DW | 18.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wulff a ƙasar Turkiya

Ziyarar shugaban Jamus a Turkiya a lokacin da muhauwar kan sajewar baƙi a Jamus ta yi zafi

default

Tutocin Jamus da Turkiya

A wannan Litinin shugaban Tarayyar Jamus, Christian Wulff yake wata ziyarar aiki ta kwanaki biyar a Turkiya a daidai lokacin da muhawara game da sajewar 'yan asalin Turkiya a Jamus ta yi zafi. Wulff zai gana da takwaransa na Turkiya Abdullah Gül, kana zai yi jawabi a gaban majalisar dokokin Turkiya. A wani jawabi da ya yi a farkon wannan wata, shugaba Wulff ya shiga kanun labaru inda ya ce addinin Musulunci kamar Kiristanci da Yahudanci wani ɓangare ne na Jamus. Firimiyan jihar Bavariya mai ra'ayin mazan jiya, Horst Seehofer ya mayar da martani da cewa Jamus ba ta buƙatar ƙarin baƙi daga ƙasashe masu bin wasu al'adu daban musamman daga ƙasashen Larabawa da Musulmai. Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a jawabin da ta yi a ƙarshen mako ta yi nuni da cewa ƙoƙarin samar da wata al'umma mai bin al'adu daban-daban a Jamus ya ci tura. A nasa ɓangare shugaban jam'iyar The Greens, Cem Özdemir ya yi kira ga shugaba Wulff da ya guji abubuwan da za su karkata hankalinsa yayin wannan ziyara a Turkiya da ke zama irinta ta farko da wani shugaban Jamus ya kai ƙasar a cikin shekaru 10 kuma ake ganinta a matsayin wani gwaji na shugabancinsa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas