Wolfowitz ya yarda zai yi murabus. | Labarai | DW | 18.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wolfowitz ya yarda zai yi murabus.

Shugaban Bankin duniya Paul Wolfowitz ya amince ya sauka daga mukamin sa a ƙarshen watan Yuni mai kamawa. Hakan ya biyo bayan wallafa wani rahoton bincike na musamman wanda ya baiyana Wolfowitz da cewa ya keta dokokin tsarin aikin Bankin. Wolfowitz dai ya faɗa wadi na tsaka mai wuya ne inda aka yi ta masa matsin lamba ya sauka daga mukamin sa, sakamakon karin albashi da ya yiwa budurwar sa wanda ya wuce ƙima. Kakakin shugaban Amurka George W Bush yace nan ba da jimawa ba shugaban na Amurka zai baiyana sunan wanda zai maye gurbin Wolfowitz a matsayin shugaban Bankin duniyar. Ministan kuɗi na nan Jamus Peer Steinbrück yace Wolfowitz ya yi farar dabara da ya yi murabus domin taɓargazar da ya ƙwaɓa ta zubar da mutuncin Bankin duniyar.