Wolfowitz ya shiga ukku | Labarai | DW | 27.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wolfowitz ya shiga ukku

Jami´an yaƙi da cin hanci da rasahawa a bankin dunia na ci gaba da matsa ƙaimi ga shugaban bankin dunia Paul Wolwofitz da ya yi murabis daga muƙanmin sa.

Hakan ya biwo bayan sakamakon abun kunyan nan, da ya tabka na ware kuɗaɗen albashi masu toska, ba bisa ƙa´ida ba, ga wata budurwa sa da ke aiki a bankin dunia.

Idan dai ba amnta ba ranar laraba da wwuce yan majalisar dokokin ƙungiyar gamaya turai, suma sun bayyana irin wannan buƙata.

To saidai bisa dukkan alamu, Paul Wolwofitz da ya samu ɗaurin gindin daga shugaba Bush na Amurika, zai ci gaba da jagorancin wannan banki.

A cikin wata sanarwa da su ka bayyana, jami´an yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa an Bankin Dunia, sun nunar da cewa, abun kunya da Wolfowitz ya aikata, babban lefi ne mai nasaba da cin hanci da karbar rashawa, a game da haka ya zama wajibi ya sauka daga wannan mukami, muddun a na bukatar kare ƙima da darajar bankin a idanun dunia.