Wilma tayo kasa daga mataki na hudu izuwa biyu | Labarai | DW | 24.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wilma tayo kasa daga mataki na hudu izuwa biyu

Bayanai daga kasar Amurka na nuni da cewa mahaukaciyar guguwar nan ta wilma ta sakko daga mataki na hudu a yanayi na karfi da take tafiya izuwa mataki na biyu.

Bugu da kari bayanan sun kuma tabbatar da cewa duk da wannan raguwa da guguwar tayi har yanzu tana ci gaba da mamaye jihar Florida, a inda bayanai suka yi nuni da cewa tana tafiyar kilomita 175 a cikin awa daya.

Kafin dai raguwar guguwar ta Wilma izuwa mataki na biyu, rahotanni sun shaidar da cewa tayi ta´adi mai munin gaske a inda a yanzu haka ta bar mutane sama da dubu dari uku babu gidajen kwana.