1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wilma ta fara barna a birnin Florida na kasar Amurka

October 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvO3

Mahaukaciyar guguwar nan ta wilma a yanzu haka ta isa birnin Florida na kasar Amurka. Bayanai sun shaidar da cewa wannan mahaukaciyar iasaka ta wilma ta tafiyar kilomita 185 a cikin awa guda.

Bugu da kari bayanai sun shaidar da cewa dubbannin mutanen birnin tuni kowa ya samu mafaka don gudun kada guguwar tayi tafiyar ruwa dashi.

Har ilya yau bayanai daga birnin sun tabbatar da cewa wannan guguwa tayi mummunan ta´adi a tsibirin keys, a inda ta lalata gidajen kwana da kuma ofisoshin hada hadar kasuwanci.

Ya zuwa yanzu dai masu nazarin yanayi sun shaidar da cewa wannan guguwa ta wilma a yanzu haka na a mataki na uku ne a yanayi na karfi da take tafiya .