1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

WHO TA NUNA DAMUWARTA KAN YADUWAR MAGUNGUNAN JABU A DUNIYA.

Hukumar lafiya ta duniya, wato WHO a takaice, ta yi gargadin cewa, ana ta kara samun habakar yawan magungunan jabu da ake sarrafawa a duniya. Wadannan magungunan dai ba su da wani amfani, suna kuma da illoli. A wasu lokutan ma, suna iya janyo salwantar rayukan wadanda ke amfani da su. Hukumar ta yi wannan gargadin ne a wani kamfen da ta kaddamar, a kudu maso gabashin Asiya, don yakan yaduwar magungunan jabun, wadanda a wannan yankin ne aka fi sarrafa su.
Bisa alkaluman da hukumar ta buga dai, kusan kashi 25 cikin dari na magungunan da ake sha a kasashe masu tasowa, da nufin warkad da miyagun cututtuka kamarsu maleriya, da tibi, da AIDS, ba na kwarai ba ne, ko kuma ba sa cika ka'idojin da aka ajiye na sarrafa su. A kasashe mawadata ma, a kan sami irin wannan matsalar, na yaduwar magungunan jabu. Hukumar ta WHO, ta bayyana cewa, maganin da aka fi kwaikwayon sarrafa shi a wadannan kasashen shi ne Viagra, wanda ya shahara saboda kara mazakutan da aka ce yana yi. A halin yanzu ana iya sayen wannan maganin ta hanyar Internet. A nan ne kuma kasadar take, saboda masu sayen, ba su da wata hanyar tabbatad da sahihancinsa. Hukumar lafiyar ta duniya dai, ta gargadi jama'a da su guji sayan duk wasu magunguna ta wannan hanyar.
Kamar yadda darekta-janar na Hukumar Lafiyar Ta Duniya, Lee Jong-wook, ya bayyanar, a halin yanzu yakan sarrafa haramtatttun magunguna da kasuwancinsu, shi ne gurin da hukumar ta fi bai wa muhimmanci a cikin manufofinta. Kamata ya yi, a dau duk matakan da suka dace wajen bai wa jama'a damar samun sahihan magunguna don warkad da cututtuka kamarsu AIDS da dai sauransu, inji Lee.
Wani jami'in hukumar mai kula da fasahohi, Clive Ondari, ya bayyana cewa a ko wace shekara, kusan mutane miliyan daya ne ke mutuwa saboda kamuwarsu da cutar maleriya. Daga cikin wannan adadin kuwa, mutane dubu dari 2 na mutuwa ne saboda shan magungunan jabu.
Hukumar sa ido kan magunguna da abinci na Amirka, wato FDA, ta kiyasci cewa, yawan magungunan da ake kwaikwayon sarrafa su a duniya a halin yanzu, ya kai kashi 10 cikin dari na duk magungunan da ake kasuwancinsu a duniya baki daya. Cinkin da ake yi a kan wannan nau'in kawai, wato na magungunan jabun, ya kai kimanin dolar Amirka miliyan dubu 32.
Wani binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gudanar, tsakanin watan Janairun 1999 zuwa watan Oktoba na shekara ta 2000, ya nuna cewa ana samun kusan kashi 60 cikin dari na magungunan jabun ne a kasashe masu tasowa, sa'annan kashi 40 cikin dari kuma a kasashe masu ci gaban masana'antu.
Saboda tsanantar wannan matsalar da kuma yadda masu sarrafa magungunan jabun ke cin karensu babu babbaka ne Hukumar Lafiya Ta Duniya da wasu kafofi na kasa da kasa, suka shirya wani taro na kwana 3 a birnin Hanoi na kasar Vietnam don tattauna yadda za a shawo kan wannan matsalar, musamman ma dai a kasashen Cambodiya, da Sin, da Laos, da Myanmar da Thailand da kuma Vietnam din da kanta. A wadannan kasashen ne dai aka fi sarrafa magungunan jabun.
Wani kakakin hukumar lafiya ta duniya ya bayyana cewa, gurin da taron ya sanya a gaba ne, zartad da kuduri wanda zai bai wa kasashe damar fatattakar masu gudanad da wadannan miyagun ayyukan, da inganta hanyoyin sa ido kan kasuwancin magunguna don gano na jabu kai tsaye, da kuma fadakad da jama'a kan barazanar da shan ire-iren wadannan magungunan zai iya yi wa koshin lafiyarsu.
Shugaban reshen fasahar kiwon lafiya da na sarrafa magunguna na Hukumar Lafiya Ta Duniya, Vladimir Lepakhin, ya ce akwai hanyoyi da yawa na inganta magunguna da sa ido kan hanyoyin sarrafa su da kuma yadda za a rarraba su. Amma babbar matsalar da akwai ita ce, kasashe masu tasowa ba su da kafofin aiwatad da wasu matakan, alhali kuma su ne ke ta fama da yawan cututtuka da matsalolin tattalin arziki.
A bangaren kasashe masu arzikin masana'antu kuwa, matsalar ta shafi kasuwancin magungunan ne da ake yi ta hanyar Internet. A nan kuwa, jami'an sa ido na huskantar matsloli ne wajen bin sahun masu keta dokokin.

 • Kwanan wata 12.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvne
 • Kwanan wata 12.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvne