1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Westerwelle ya yi kira da a ɗage tarnaƙi kan Gaza

November 8, 2010

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya kai ziyara a Zirin Gaza

https://p.dw.com/p/Q1j7
Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle tsaye a tsakiya ɗalibai mata 'yan gudun hijira a wani aji lokacin ziyararsa a makarantar Al Shatea dake Zirin GazaHoto: picture alliance/dpa

Guido Westerwelle shi ne wani babban jami'in gwamnatin Jamus na farko da ya kai ziyara wannan yanki tun a shekarar 2006, ya ganewa idonsa wata makaranta ta Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma wani wurin tace ruwan sha da Jamus ta ba da kuɗin ginawa. A gaban 'yan jaridar, Westerwelle ya yi kira ga gwamnatin Isra'ila da ta ƙara sauƙaƙa takunkumin da ta ɗora kan Gaza kana kuma ta ba da izinin shiga da kayakin kasuwanci wannan yanki. Tun a shekarar 2007 Isra'ila ta sanya tarnaƙi ga yankin Zirin Gaza dake ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas. A lokaci ɗaya kuma ministan harkokin wajen na Jamus ya yi kira da a sako sojin Isra'ilan nan Gilad Shalit wanda aka sace shekaru huɗu da suka wuce. Tun dai a jiya Westerwelle ya gana da takwaran aikinsa na Isra'ila Avigdor Lieberman, inda ya buƙaci Israila da Falasɗinawa su ruɓanya ƙoƙari ga samun nasarar tattaunawa kai tsaye ta wanzar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, yana mai cewa bai kamata a riƙa samun tsaiko a shirin tattaunawar ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas